in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar MDD ta fara binciken fashewar da ta faru a gabashin DRC
2016-11-09 10:23:16 cri

Tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar demokiradiyar Congo DRC ta fara gudanar da bincike game da musabbanin wata mummunar fashewa da ta halaka wata yara yarinya, tare da jikkata ma'aikatan da ke aikin wanzar da zaman lafiya na majalisar 'yan kasar Indiya jiya a gabashin kasar.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar majalisar cewa, ma'aikatan da ke aikin wanzar da zaman lafiya biyar ne suka ji mummanan rauni a fashewar da ta auku a garin na Goma.

Rahotanni farko-farko sun bayyana cewa, fashewar wadda ta auku yayin da ma'aikatan suke motsa jiki da suka saba yi a ko wace safiya ta faru ne sakamakon matsalar na'ura.

Tuni dai ofishin tawagar MDD da ke Jamhuriyar demokiradiyar Congo (MONUSCO) ya aike da dakarun kota-kwana gami da tawagar bincike, da kwararrun masu kwance abubuwan fashewa. zuwa wurin da lamarin ya faru.

Ana sa ran wakilin magadakardan MDD a DRC Maman Sambo Sidikou zai yi tattaki zuwa garin Goma domin ganewa idon sa abubuwan da suke faruwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China