in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci DRC ta fidda jadawalin gudanar da zaben kasar
2017-10-12 10:02:06 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci hukumomin jamhuriyar demokaradiyyar Congo (DRC), da su hanzarta fitar da jadawalin zabukan kasar, wanda ake sa ran hakan zai iya zama matakin farko na sauya shugabancin kasar cikin kwanciyar hankali.

Francois Delattre, jakadan Faransa a MDD, wanda kuma shi ne jagoran kwamitin tsaron MDD a watan Oktoba ya ce, kwamitin tsaron yana sa ran za'a fitar da ranakun gudanar da zabukan, da kuma aiwatar da muhimman matakan da za su tabbatar da samun nasarar shirya zaben.

Bayan wani taron sirri na kwamitin tsaron, Delattre ya shedawa 'yan jaridu cewa, kwamitin tsaron MDD mai wakilan kasashe 15, ya amince a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2016, wadda ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da sahihin zabe mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali a DRC.

Yarjejeniyar ta baiwa shugaba Joseph Kabila na DRC dama, wanda ya dade kan karagar mulkin kasar tun a shekarar 2001, inda zai ci gaba da zama a madafun iko bayan da wa'adin mulkinsa ya kare, kasancewa sharadin ya nuna cewa, dole a shirya zabuka a wannan shekara ta 2017. Sai dai a bisa dukkan alamu ba lallai ne a gudanar da zaben kasar a cikin wannan shekarar ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China