Wakiliyar MDD ta bayyana damuwa game da yanayin tabarbarewar al'amurran siyasa da tsaro da yanayin rayuwar bil adama a jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC, duk kuwa da ci gaban da aka samu game da shirye-shiryen gudanar da zabuka a kasar.
Da take jawabi ga kwamitin sulhun MDD, Leila Zerrougui, wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD a DRC, ta bayyana cewa, an samu gagarumin ci gaba a 'yan makonnin da suka gabata a shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisun dokoki, ciki kuwa har da batun kammala aikin rijistar masu zabe.
Sai dai kuma ta yi gargadin cewa, har yanzu akwai wasu manyan kalubaloli da suka dabaibaye kasar.(Ahmad Fagam)