in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya soki hari kan sansanin MONUSCO a DRC
2015-12-01 09:29:49 cri

A ranar Litinin din nan kwamitin tsaro na MDD ya soki harin da 'yan tawayen Uganda suka kai a sansanin tawagar wanzar da zaman lafiya dake jamhuriyar demokradiya ta Congo DRC MONUSCO.

Wannan harin da dakarun ADF dake arewacin Kivu a gabashin DRC suka kai ya yi sanadiyar mutuwar ma'aikacin wanzar da zaman lafiya guda daya 'dan asalin kasar Malawi, sojoji 4 na rundunar sojin Congo, da wassu fararen hula da dama, sannan kuma wadansu sun samu rauni, ciki har da ma'aikacin ofishin guda daya.

Kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa, kwamitin ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan ma'aikacin da ya rasu, da gwamnatin kasar Malawi da kuma tawagar ta MONUSCO, da ma ita kanta gwamnatin kasar ta DRC.

Kwamitin ta soki harin da kakkausar murya wanda dakarun ADF a arewacin Kivu, ke yawan aikata shi galibi a kan fararen hula da a yanzu haka mutane sama da 500 suka halaka tun daga watan Oktoban bara.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China