in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yabawa Kasar Sin bisa kokarinta na dakile yaduwar cutar kanjamau
2018-06-22 15:42:36 cri
Babban Daraktan hukumar MDD (UNAIDS) mai yaki da cutar kanjamau Michel Sidebe, ya ce bisa kyakkyawan shugabanci da basira da hadin gwiwa, kasar Sin ta samu gagagrumar nasara wajen yaki da cutar kanjamau.

A cewar cibiyar takaita yaduwa da yaki da cutar Kanjamau ta kasar Sin, Ya zuwa watan Satumban bara, kasar Sin na da jimilar mutane 747,000 dake dauke da cutar, kuma kawo karshen watan Yuni, kusan 542,000 na karbar magani.

Darktan ofishin hukumar a kasar Sin Amakobe Sande, ya ce irin kokarin Kasar Sin na yaki da cutar kanjamau abun ne da ba a saba gani ba, la'akari da yawan al'ummarta. Ya kara da cewa, abun da yake burge shi da kasar Sin shi ne, idan ta sa wani buri a gaba, to sai ta cimma masa.

Domin samun al'umma mai lafiya ne a shekarun baya-bayan nan, kasar Sin ta kaddamar da gangamin yaki da cutar kanjamau. inda ya zuwa karshen 2017, kasar ta kusan dakile yaduwar cutar ta hanyar karin jini kuma ta takaita yaduwarta ta hanyar amfani da allura da kuma wanda ake samu daga uwa zuwa da yayin rainon ciki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China