Mambobin mazhabar shi'ar sun gudanar da wata zanga-zanga a jiya Alhamis, domin nuna adawa da tsare shugabansu Ibrahim El-Zakzaky da wasu mambobin kungiyar da Gwamnatin kasar ke ci gaba da yi.
Al'amarin ya auku ne a lokacin da El-Zakzaky da matarsa Zeena suka bayyana gaban kotu a tsakiyar garin.
Sai dai ba a yi zaman shari'ar ba saboda rashin zuwan alkalin dake shari'ar.
An yi zargin an yi ta jifan dan sanda har ya mutu lokacin arangamar, inda kuma aka kona wata motar sintiri ta 'yan sanda a unguwar Kano road dake birnin.
Gwamnatin jihar Kaduna ce ta gurfanar da El-Zakzaky a gaban kotu, inda ta ke tuhumarsa da laifuka 8 da suka hada kashe-kashe da tattaki ba bisa ka'ida ba da kuma damun al'umma. (Fa'iza Mustapha)