in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya zasu fara shirin farautar 'yan bindiga a arewa maso yammacin kasar
2018-06-19 09:48:55 cri
Sojojin Najeriya zasu fara wani shirin hadin gwiwa domin murkushe ayyukan 'yan bindiga a jahar Zamfara a arewa maso yammacin kasar, kamar yadda sojojin saman Najeriya suka tabbatar.

Kwamandan rundunar kai daukin gaggawa na runduna ta 207, Caleb Olayera, ya fada a Gusau babban birnin jahar Zamfara cewa, shirin hadin gwiwar tsakanin dakarun sojin ya kunshi sojojin sama, dana kasa, da 'yan sanda, da jami'an tsaron farin kaya don murkushe 'yan bindigar.

Kwamandan sojin ya bayyana hakan ne bayan tura wasu jiragen saman yakin soji guda biyu wadanda za'a yi amfani dasu.

Jahar Zamfara ta jima tana fama da matsalar hare haren 'yan bindiga inda yayi sanadiyyar hallaka daruruwan jama'a, kana ya tilastawa dubban jama'a yin kaura daga yankunansu.

Olayera ya bada tabbacin samar da zaman lafiya a sassan jahar ta Zamfara da zarar an fara aikin sintirin sojojin na hadin gwiwar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China