in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta musanta cewa mayakan ISIS sun shiga kasar
2018-06-22 09:46:41 cri
Hukumomin tsaro a Nijeriya, sun musanta rahotannin dake cewa kasar na karkashin barazanar wata kungiyar 'yan ta'adda dake kasar ko kasashen waje.

Sanarwar da rundunar sojin kasar ta fitar jiya, ta musanta rahotanni da kafafen yada labarai suka bayar dake cewa, kungiyar ISIS ta shiga kasar, musammam domin horar da kungiyar 'yan tada kayar baya ta Boko Haram.

Sanarwar ta ce babu wata kwakwarar shaida dake tabbatar da ikirarin cewa ISIS ta tura mambobinta domin horar da 'yan Boko Haram.

A farkon makon nan ne, kafafen yada labarai suka bada rahotannin dake cewa, kasar dake yammacin Afrika na karkashin barazanar ISIS, suna masu ruwaito wani rahoto daga jaridar Birtaniya.

Kafafen yada labaran da ba su bayyana majiyoyinsu ba, sun kara da cewa, mayakan ISIS na shiga Nijeriya daga Syria ne domin horar da 'yan tada kayar baya da nufin kai hare-hare Birtaniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China