in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na bana, duk da sauye-sauyen da aka yi ciki
2018-06-22 09:56:03 cri
Watanni 7 bayan Gwamnatin Nijeriya ta mika kudurin kasafin kudin bana ga majalisar dokokin kasar, Shugaba Muhammad Buhari ya rattaba hannu kan kasafin da ya kai naira triliyan 9.12 kwatankwacin dala biliyan 25.2, a jiya Laraba.

Shugaban wanda ya rattaba hannu a Abuja babban birnin kasar, ya bayyana damuwa game da sauye-sauyen da majalisar ta yi kan kudurin kasafin.

A ranar 26 ga watan Oktoban 2017 ne, majalisar zartarwar kasar ta amince da daftarin kaasafin kudin na naira triliyan 8.61, sai dai majalisar dokokin kasar ta kara kudin zuwa naira triliyan 9.12.

Majalisar ta kuma kara adadin da aka kayyade cikin kasafin na danyan man fetur daga dala 45 kan kowacce ganga, zuwa dala biliyan 50.5.

Shugaba Buhari ya bayyana damuwa game da yadda majalisar ta rage kudin da ya kai naira biliyan 347 na ayyuka 4,700 da ya aike musu domin amincewa, kuma suka saka wasu ayyuka 6,403 da kudinsu ya kai naira biliyan 578.

Ya kara da cewa, ayyukan da majalisar ta zaftare kudaden aiwatar da su na da muhimmanci, kuma za su yi wuyar aiwatarwa da kudaden da suka sanya . (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China