in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya na da yakinin kungiyar Super Eagles za ta samu cancanta a rukunin da take
2018-06-19 10:19:24 cri
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF Amaju Pinnick, ya ce har yanzu kungiyar kwallon kafar kasar wato Super Eagles, na da damar samun nasara a rukunin da take a wasan kwallon kafa na cin kofin duniya dake gudana a Rasha.

Amaju Pinnick ya bayyna cewa, duk da doke Super Eagles din da Croatia da yi da ci 2 da nema, akwai yiwuwar kungiyar ta tabuka abun azo a gani a rukunin na D.

Amaju Pinnick, ya kuma ce babu wata kungiya a rukunin na D da za ta bugi kirjin samun cancanta, yana mai cewa akwai yiwuwar abubuwa da dama a wasan kwallon kafa, muddun akwai burin samun nasara.

Shugaban da sauran mambobin majalisar zartarwar hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, sun kuma yi kira ga 'yan Nijeriya dake gida, su ci gaba da marawa kungiyar baya da kyawawan kalamai.

Kungiyar Super Eagles ta koma sansaninta na Essentuki a ranar Lahadin da ta gabata, kuma tuni 'yan wasan suka fara atisayen shirya tunkarar wasan da za a yi ranar Juma'a a filin wasa na Volgogard. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China