Cikin kasidar mai taken, "Yadda Amurka ta yi hasara: Kasar Sin tana kara samun bunkasar matsayi a Afrika," ance "Kasar Sin tana kara taka muhimmiyar rawa a harkokin tattalin arzikin duniya da kuma cigaba, cikin kasashen har da Afrika" yayin da kuma kasar dake da al'adar bada taimako kamar Amurka a halin yanzu bata da wani kwakkwaran buri akan Afrika kuma matsayin Amurkar yana kara samun koma baya a nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)