Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ya ruwaito Guterres yana mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda tashin hankalin na ranar Talata ya shafa, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Guterres ya kuma yi kira ga hukumomi da su gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a hare-haren don su gurfana a gaban kuliya, yana mai cewa bai ga dalilin tayar da rikici ko furta wasu kalaman nuna kiyayya ba.
A don haka ya sake nanata kudurinsa na goyon bayan gwamnatin kasar da ma matakan da tawagar ta MINUSCA ke dauka wajen kare rayukan fararen hula da samar da zaman lafiya a kasar. Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. (Ibrahim Yaya)