Tun a jiya Alhamis babban sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya bada tabbacin daukar matakan tabbatar da tsaro, bayan da gwamnatin kasar ta ayyana ranakun Juma'a 15 ga wata da kuma ranar Litinin 18 ga wata a matsayin hutu a duk fadin kasar, don baiwa jama'a damar gudanar da bukukuwan karamar sallar ta shekarar 2018, bayan da al'ummar musulmi suka kammala azumin watan Ramadan.
A wata sanarwa da sifeton 'yan sandan Najeriyar ya fitar, wanda aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya bada umarnin tura jami'an 'yan sanda zuwa sassan kasar domin a samu damar bukukuwan cikin kwanciyar hankali.
Ana saran jami'an 'yan sanda zasu tsaurara tsaro a filayen idi da sauran muhimman wuraren taruwar jama'a a yayin bukukuwan a duk fadin kasar, ya kara da cewa, jami'an zasu gudanar da ayyukansu a wuraren da suka hada da lambunan shakatawa, da wuraren taruwar jama'a, har ma da wasu muhimman gine ginen gwamnati.
A cewarsa, an baza jami'an dake bincike a manyan titunan motar kasar da masu yaki da bata gari zuwa manyan titunan mota a duk fadin kasar, kuma zasu gudanar da ayyukansu cikin natsuwa da kyakkyawar halayya a yayin da suke bakin aikinsu.
Idris yace 'yan sanda zasu gudanar da bincike a dukkan wuraren da bata gari ke fakewa a duk fadin kasar don dakile muggan laifuka.