in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan kungiyar Changchun Yatai ya bayyana kwarin gwiwar sa game da nasarar tawagar Super Eagles
2018-06-08 10:30:22 cri

Dan wasan kwallon kafar Najeriya dake wasa a kungiyar Changchun Yatai dake nan kasar Sin Odion Ighalo, ya bayyana kwarin gwiwar sa, game da nasarar da yake fatan tawagar Super Eagles ta Najeriyar za ta samu, a wasannin da za ta buga na cin kofin duniya da ake daf da farawa a Rasha.

Odion Ighalo ya bayyana hakan ne, yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba, yana mai cewa yana da kyakkyawan fatan Super Eagles za ta kai ga wasannin rukuni na biyu na kasashe 16 a gasar ta bana.

Najeriya dai za ta kece raini ne da kasashen Argentina, da Iceland da kuma Croatia, a rukunin farko na gasar, kafin kaiwa ga rukunin kasashe 16 a gasar ta cin kofin duniya.

Ighalo ya kara da cewa, tun yana karami yake mafarkin buga gasar cin kofin duniya. Ya kuma taka leda a gasar ta rukunin matasa, kuma a karon farko zai shiga a dama da shi, a ajin kwararru na gasar ta cin kofin duniya, a gasar da za a bude nan da 'yan kwanaki a Rasha.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China