in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afirka da su fito da manufofin bai daya don karfafa hulda da Sin
2018-05-29 09:37:02 cri
Tsohon jakadan kasar Kenya a kasar Koriya ta kudu, Ngovi Kitau, ya ce akwai bukatar kasashen Afirka su fito da manufa ta bai daya yayin hadin gwiwar da za su yi da kasar Sin a nan gaba.

Kitau wanda ya bayyana hakan cikin wani sharhi da ya rubuta a jaridar Star wanda aka wallafa a jiya Litinin, ya kuma jaddada cewa, akwai bukatar shugabannin Afirka su bayyana inda nahiyar ta dosa kan alakar dake tsakanisu da kasar Sin gabanin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) karo na 7 da zai gudana a wata Satumban wannan shekara a birnin Beijing na kasar Sin.

Ya ce, kasashen na Afirka suna da damar yin bitar alakarsu da manyan kasashe,bisa la'akari da irin muhimman abubuwan dake faruwa a harkokin duniya. Ya ce yanzu kasar Sin ce ke taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma kasa ce da ke mutunta da kuma taimakawa sauran kasashe.

Tsohon jakadan ya kuma yaba da ci gaban da aka samu tun bayan taron dandalin na FOCAC na watan Disamban shekarar 2015 da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu,wadanda suka hada da inganta alakar cinikayya tsakanin Sin da Afirka da karfafawa shugabannin nahiyar gwiwar shiga bankin gina kayayyakin more rayuwa na Asiya da kasar Sin ta kirkiro(AIIB).

Haka kuma ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta kirkiro ita ma za ta taimakawa sabon yankin cinikayya cikin 'yanci na Afirka da aka kaddamar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China