in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Chadi, Sudan, Nijar, da Libya sun cimma wata yarjejeniyar yaki da ta'addanci da sumogal
2018-06-05 18:38:09 cri
Bisa nuna damuwa sosai kan matsalar rashin tsaro dake kamari a yankin Sahel a shekarun baya bayan nan, kasashen Chadi, Sudan, Libiya da Nijar sun cimma wata yarjejeniyar kulla huldar hadin kai ta fuskar tsaro.

Ga wadannan kasashe hudu, abu mafi jan hankali shi ne batun tsaro bisa wannan yarjejeniya da aka sanyawa hannu a ranar 31 ga watan Mayun da ya gabata, domin tsaron kan iyakokin kasashen bi da bi ta hanyar amfani da kayayyakin aiki yadda ya kamata, da yaki da ta'addanci da kuma fasa kauri da kungiyoyi masu dauke da makamai suka yi karin suna kan aikata irin wadannan manyan laifuffuka, wadanda a cikinsu akwai kungiyar Boko Haram ta Najeriya. Haka kuma kasashen hudu sun dauki niyyar hada karfi da karfe wajen yin musanyar bayanai da kuma baiwa junansu damar farautar mahara har cikin harabar kowane daga cikinsu.

Wadannan kasashe har ma da wasu kasashen Afrika suna fama da matsalar ta'addanci da kuma sumogal iri daban daban a cikin 'yan shekarun baya. A cewar kwararru, kudancin Libiya ya zama wata matattarar 'yan sumogal, a yayin da Nijar, musammun yankin Agadez ya zama hanyar da bakin haure suke dauka ba bisa doka ba domin isa kasashen Turai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China