in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijar ya gana da sabbin mambobin hukumar CSC
2018-05-17 16:20:57 cri

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya yi wata ganawa a ranar jiya Laraba, 16 ga watan Mayun shekarar 2018 tare da sabbin mambobin hukumar sadarwa ta kasa CSC da aka gudanar da zaben su a ranar 4 ga watan Afrilun da ya gabata. Bayan wannan ganawa, shugaban hukumar CSC, dokta Kabir Sani ya bayyana wa 'yan jarida cewa wata dama ce na mambobin dindindin hudu na CSC tabo muhimman batutuwan dake da nasaba da aikin kafofin yada labarai na gwamnati da masu zaman kansu a Nijar tare da shugaban kasa, musamman ma game da girmama ka'idodin aikin jarida. Mun tabbatarwa shugaban kasa girmama doka, da kuma ka'idodin aikin jarida, in ji dokta Kabir Sani. A cewarsa kuma shugaban kasa ya yi musu alkawarin kawo tallafin da ya dace domin ci gaba wata jarida mai cikakken 'yanci a Nijar. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China