in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijar na ziyarar aiki a kasar Faransa bisa goron gayyatar shugaba Macron
2018-06-04 17:27:52 cri
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya bar birnin Yamai a jiya Laraba 3 ga watan Junin shekarar 2018 zuwa birnin Paris na kasar Faransa bisa wata ziyarar aiki ta kwanaki uku bisa goron gayyatar Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa. Shugaba Issoufou ya samu rakiyar wata babbar tawaga da ta hada da ministan harkokin waje Kalla Hankouraou, ministan kudi Hassoumi Massaoudou, ministan tsaro Kalla Moutari da kuma ministan shari'a Marou Amadou.

A cewar jakadan Faransa dake Nijar bayan wata ganawa da shugaba Issoufou ya bayyana cewa, ziyarar ta shugaban Nijar na da muhimmancin gaske ganin cewa zata taimakawa wajen karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma za ta bada damar sanya hannu kan wata yarjejeniyar tallafin kudi tsakanin kasar Nijar da kungiyar AFD ta kasar Faransa domin cigaban aikin hadin kai da ya shafi kudin Euro miliyan 50. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China