in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na sa ran ganin shugabannin Koriya ta Arewa da Amurka za su gana da juna
2018-06-02 20:34:37 cri

Kasar Sin ta bayyana fata, tare da goyon bayan kokarin Koriya ta Arewa da Amurka, na ganin sun tattauna da juna.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wadda ta bayyana haka a yau Asabar, ta ce bangaren Sin na goyon bayan shirye- shiryen da Koriya ta Arewa da Amurka ke yi na taronsu dake karatowa.

A jiya Juma'a ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, zai gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ranar 12 ga watan nan a Singapore, kamar dai yadda aka tsara a baya kafin ya soke ganawar.

Hua Chunying ta jadadda cewa, yanayin da ake ciki yanzu game da zirin Koriya na cikin wani muhimmin mataki na tarihi da ba a saba gani ba. Ta ce, taron tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa na da muhimmanci ga kawar da makaman nukiliya da samar da zaman lafiya mai dorewa a zirin.

Ta kara da cewa, kasar Sin na sa ran Koriya ta Arewa da Amurka za su cimma matsayar da dukkansu da kuma al'ummomin duniya ke muradi, ta yadda za a bude sabon babi na kawar da makaman nukiliya da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China