in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce mai yiwuwa a samu jinkiri a ganawarsa da shugaban DPRK
2018-05-23 10:08:26 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Talata cewa, wata kila za'a iya samun jinkiri a ganawar da aka shirya yi tsakaninsa da takwaransa na Koriya ta Arewa (DPRK) Kim Jong Un.

"Mai yiwuwa ba za'a yi tattaunawar ba a ranar 12 ga watan Yuni." Trump ya fadawa 'yan jarida a fadar White House a lokacin da yake ganawa da shugaban Koriya ta kudu (ROK) Moon Jae-in, wanda ke ziyara a kasar Amurkar, inda shugaba Trump yake buga misali da ranar da aka shirya ganawa da mista Kim.

Dama dai DPRK ta yi barazana a makon jiya cewa, mai yiwuwa Pyongyang din ba za ta amince ta halarci ganawar da aka shirya yi a Singapore ba, muddin dai Amurka tana burin yiwa Koriya ta arewar matsin lamba ne kawai domin ta yi watsi da shirinta na nukiliya.

Pyongyang ta yi watsi da tattaunawar da aka shirya gudanarwa tsakanin Koriyoyin biyu a ranar Larabar makon jiya, inda ta nemi a yi watsi da shirin atisayen soji mafi girma na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Koriya ta kudu, kana ta kuma bukaci ROK da ta dakatar da shirin atisayen sojin hadin gwiwar da Amurka.

Sai dai fadar White House da ma'aikatar harkokin wajen Amurka sun sanar a makon jiya cewa, za su ci gaba da shirye shiryen ganawar da za'a gudanar tsakanin Trump da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China