in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump zai gana da Kim a Singapore kamar yadda aka tsara
2018-06-02 15:39:17 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai gana da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a ranar 12 ga watan nan a Singapore, kamar dai yadda aka shirya a baya.

Donald Trump ya bayyana haka ne jiya a fadarsa ta White House, bayan ganawar da ya shafe kusan sa'o'i 2 yana yi da babban jami'in Pyongyong, wanda ya kai masa wasika ta musammam daga shugaba Kim.

Bayan ganawarsa da Kim Yong Chol, mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar 'yan kwadago mai mulkin Koriya ta Arewa, shugaban na Amurka ya shaidawa manema labarai cewa, Washington da Pyongyang za su kulla huldar da za ta fara aiki a ranar 12 ga watan Yuni.

Babban jami'in na Koriya ta Arewa, ya shafe yini 2 yana ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, a birnin New York, kafin ya wuce Washington a jiya Juma'a.

Donald Trump ya kuma bayyana ganawar da za su yi da shugaban Koriya ta Arewa a matsayin wani yanayi na fahimtar juna, yana mai cewa, ya yi ammana Koriyar tana son kawar da makaman nukiliya.

Ya kara da cewa, yana da yakinin za a samu kyakkyawan sakamako a karshe, inda ya ce, akwai bukatar gudanar da taro fiye da daya, la'akari da tsawon shekaru da aka shafe kasashen na dabi da juna.

Bugu da kari, Trump ya ce, yayin ganawarsa da Kim Yong Chol, sun tattauna kan takunkuman da Amurka ta kakabawa Koriya ta Arewa.

A nasa bangaren, jami'in na Koriya, ya ce ba ya son ya sake yin amfani da kalmar 'matsin lamba' tun da kasashen biyu na kokarin warware sabanin dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China