in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce yana sa ran ganawa da Kim a 12 ga Yuni
2018-05-27 15:29:16 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Asabar cewa, yana fatar halartar taron kolin Singapore domin ganawa da shugaban kasar Koriyar ta Arewa Kim Jong Un, a ranar 12 ga watan gobe.

Shugaba Trump ya shedawa 'yan jaridu a fadar White House cewa, "Muna fatar halartar taron Singapore a ranar 12 ga watan Yuni. Ba za'a fasa ba", ya kara da cewa, ana samun ci gaba game da batun tattaunawar da aka tsara gudanarwa.

Ya ce, suna iya yin dukkan abin da ya dace game da batun taron kolin. Kuma komai yana tafiya yadda ya kamata.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Trump ya ba da sanarwar soke taron ganawar, inda ya bayyana cewa, ba za'a yi ganawar ba saboda abin da ya kira da cewa, abin bakin ciki da takaici wanda Koriya ta Arewa ta nuna cikin wasu kalamanta da ta fitar a kwanakin baya.

To sai dai kuma, shugaban na Amurka ya sauya matsayinsa kwana guda bayan sanarwar da ya fitar. Dukkannin bangarorin biyu suna fatan ganin an gudanar da taron ganawar, kuma za'a gudanar da taron tattaunawar bayan kyakkyawar matsayar da aka cimma.

Mai maganar fadar White House ta sanar a jiya Asabar cewa, tawagar jami'an Amurka za ta ziyarci kasar Singapore a karshen wannan makon kamar yadda aka tsara, domin yin shirye shiryen da suka dace game da taron tattaunawar ta shugaba Trump da Kim za su yi.

Yan sa'o'i kadan da suka gabata, kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewan ya sanar da cewa, shugaban Kim ya bayyana cewa, matsayinsa bai canza ba na amincewa da halartar taron tattaunawar, bayan wani taron ganawa da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in a ranar Asabar a kauyen Panmunjom.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China