in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
White House: Amurka ba ta ayyana yaki a kan DPRK ba
2017-09-26 09:53:47 cri

Mai magana da yawun fadar Amurka ta White House Sarah Sanders ta ce, Amurkar ba ta ayyana yaki a kan Koriya ta arewa wato DPRK ba, domin mayar da martini kan kalaman da babban jami'in difilomasiyar Koriyar ta arewan ya yi.

Sanders ta ce, manufar Amurka kan Koriya ta arewa ba ta canja ba, don haka za su ci gaba da lalubo matakan kawar da makaman nukiliyar zirin Koriya cikin lumana.

A makon da ya gabata ne dai, shugaba Trump na Amurka ya yi ikirarin cewa, jagororin Koriya ta arewar ba za su yi nisan kwana ba, kamar yadda ministan harkokin wajen Koriya ta arewa Ri Yong-ho ya shaidawa manema labarai a New York.

A don haka Mr Ri, ya ce, ya kamata duniya ta san cewa, sakon da Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter, na nuna cewa, Amurka ce ta fara ayyana yaki a kan kasarsa.

Wannan ne ya sa, fadar White House ta mayar da martini, inda ta karyata kalaman Koriya ta arewa dake cewa, Amurka ta ayyana yaki a kan Pyongyang.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China