in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta bunkasa fannin kudade don tallafawa kanana da matsakaitan sana'o'i
2018-05-30 09:54:48 cri
Gwamnan bankin tsakiya na kasar Sin ya sanar a jiya Talata cewa, kasar za ta dauki matakan samar da karin kudaden da za'a tallafawa kananan 'yan kasuwa da kananan sana'o'i a kasar.

Gwamnan bankin na (PBOC) na kasar Sin, Yi Gang yace, domin saukaka hanyoyin samun rancen kudade da matsananciyar bukatar kudade da kananan 'yan kasuwa da matsakaitan sana'oi ke da ita, bankin na PBOC zai yi aiki tare da sauran hukumomin da abin ya shafa domin kyautata tsare tsaren da suka dace don cimma wannan buri.

Yi ya ce, kanana da matsakaitan sana'o'i suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fannin kirkire kirkire da sana'o'in dogaro da kai, kana suna bunkasa hanyoyin samun ayyukan yi da kuma inganta yanayin zaman rayuwar al'umma. Samar da kudaden tallafi ga kanana da matsakaitan sana'o'i ya kasance wani muhimmin ginshiki a fannin kudi wanda zai taka muhimmiyar rawa ga cigaban tattalin arziki da kuma kaucewa fadawa cikin matsaloli. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China