in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nuna adawa da takalar da Amurka ke mata a yankunan ruwanta
2018-05-28 10:13:27 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana rashin jin dadin kasarsa karara game da yadda wasu jiragen ruwan yakin Amurka biyu suka shiga yankuan ruwan kasar ta Sin dake gabar tsibiran Xisha ba tare da iznin gwamnatin kasar ba.

Lu Kang wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a daren jiya, ya ce, bayan faruwar lamarin, sojojin ruwan kasar Sin sun gano jiragen ruwan yakin na kasar Amurka guda biyu suka kuma matsa musu lamba domin su bar yankin bayan an yi musu gargadi.

Lu Kang ya ce, tsibiran Xisha mallakar kasar Sin ne kamar yadda dokokin Jamhuriyar jama'ar kasar Sin game da yankunan ruwa da wuraren da ake takaddama a kansu suka nuna. A shekarar 1996 kuma gwamnatin kasar Sin ta fitar da dokar dake tabbatar da cewa, yankunan tekun dake gabar tsibiran na Xisha mallakar ta ce.

Bugu da kari, dokokin kasar Sin sun yi bayani game da haramtawa jiragen ruwan kasashen ketare shiga yankunan tekun kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China