A jawabinsa kwamitin lardin Guangdong na JKS Li Xi ya ce taron na wannan shekara, ya zo daidai da cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar kasar Sin ta zurfafa yin gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen waje. Kuma birnin Shenzhen na lardin Guangdong, a nan ne aka fara aiwatar da wannan manufa. Daya daga cikin nasarorin da aka cimma karkashin wannan manufa shi ne yankin tattalin arziki na musamman dake Shenzhen.
"Shenzhen dai dan karamin gari ne da ya shahara a fannin kamun kifi. Amma daga bisani, garin ya gawurta, kuma yanzu haka akwai kimanin gine-gine 1,000 masu tsayin sama da mita 100. " In ji tsohon shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar dattawan kasar Pakistan Mushahid Hussain Syed wanda ya taba ziyarar birnin Shenzhen a matsayin dan jarida shekaru 40 da suka gabata. (Ibrahim)