Ma'aikatar cinikin ta ce, kalaman na White House wasu irin bayanai ne wadanda bai kamata bangarorin biyu su tsammaci hakan ba, bisa abin da ake sa ran faruwarsa game da wannan batu.
MOC ta sanar a shafinta na intanet cewa, "Ko ma wanne irin mataki Amurka za ta dauka, kasar Sin tana da kwarin gwiwa, kuma tana da karfin iko da kwarewar da zata kare muradun al'ummarta da kuma moriyar kasarta".
Sanarwar ma'aikatar cinikin ta ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta zartar da abin da ya dace karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a kwanan nan. (Ahmad Fagam)