Yayin wani taro da aka yi ta bidiyo, Zhoa Kezhi, ya bukaci a ci gaba da gangamin wayar da kai domin hana ayyukan samarwa da sayar da kayan sa maye, da taimakawa masu shansa, da kuma takaita abubuwan dake da alaka da samar da kwayoyin.
Ya kara da yin kira, da a samar da tsarukan yaki da miyagun kwayoyi, ciki har da gangamin hana shan kwayoyin da kuma hadin gwiwar kasa da kasa kan takaita su.
Tuni aka fara gangamin yaki da miyagun kwayoyi cikin wannan watan a kasar Sin, inda za a yi nazarin yankunan dake fama da matsalar shan miyagun kwayoyi. (Fa'iza Mustapha)