Firayiminista kuma mataimakin shugaban kasar na daya Bakri Alhassan Saleh da wasu jami'an gwamnati da na hukumar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar da jami'an MDD da na kungiyoyin bada agaji da hukumomin da abun ya shafa da na kungiyoyin al'umm da shugabannin addinai da kungiyoyin matasa dake cikin masu samar da dabarun yaki da tsattsauran ra'ayi a Sudan, na daga cikin wadanda suka shaida kaddamar da shirin a jiya Alhamis.
Firayiminista kuma mataimakin shugabn kasar na daya, Bakri Hassan Saleh ya jadadda kudurin gwamnatin Sudan na bada hadin kai wajen yaki da tsattsauran ra'ayi a kasar.
A nata bangare, Shugabar shirin bada agajin jin kai na MDD kuma shugabar shirin UNDP a Sudan Marta Ruedas, ta ce ba kadai Sudan ayyukan masu tsattsauran ra'ayi ya shafa ba, har da nahiyar da ma duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)