Babban jami'in hukumar ya ce shirin mai suna LuQuLuQu zai mayar da hankali ne kan ilimin falsafar Afrika da ake wa lakabi da Ubuntu ko Ujama, wanda ke da nufin karfafa daukar nauyi tare da raba albarkatu bakin gwargwado da tallafawa juna, wadanda akidu ne dake kunshe cikin al'adu da halayen da 'yan Afirka suka aminta da su.
Hukumar ta ce za a kaddamar da Shirin na LuQuLuQu ne a cikin watan Nuwamba, lokaci guda a kasashe 6 na nahiyar, ciki har da Afrika ta Kudu da Nijeriya da Ghana da Ivory Coast da kuma Senegal.
Kimanin mutane miliyan 20.2 ne ke gudun hijira a Afrika. Akwai kusan rabin miliyan a Kenya, inda kimanin 489,239 daga cikinsu suka kasance mata da yara. (Fa'iza Mustapha)