Cikin sanarwar da take fitarwa bayan watanni biyu, hukumar ta ce tsakanin ranar 1 zuwa 15 ga watan nan, an mayar da 'yan gudun hijira 83 zuwa birnin Mogadishu, yayin da aka kai wasu 749 zuwa Kismayo dake kudanci Somalia.
Hukumar ta ce tun bayan kaddamar da aikin a ranar 8 ga watan Disamban 2014, adadin 'yan gudun hijirar Somalia da suka koma gida daga Kenya ya kai 73,031, ciki har da wadanda suka nemi komawa da kansu.
Ta kara da cewa, jimilar mutane 71,034 daga cikin 73,031 ne suka nemi komawa gida da kansu, daga sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake arewa maso gabashin Kenya.
Gwamnatin kasar Kenya ta ce zaman 'yan gudun hijira na ci gaba da kasancewa barazana ga tsaron kasar da ma yankin baki daya, baya ga matsalar kayakin jin kai. (Fa'iza Mustapha)