in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen Afirka su yi koyi daga kasar Sin wajen rage talauci da raya masana'antu
2017-04-02 14:04:08 cri
Wakilin shirin raya cigaban kasashe ta MDD UNDP dake kasar Sin, Nicolas Rosellini, ya bayyana kwanan baya cewa, UNDP na hadin-gwiwa tare da kasar Sin domin taimakawa kasashen Afirka samun ci gaba, wanda kuma zai kawowa juna moriya, kana, ya kamata kasashen Afirkan su yi koyi da kasar Sin ta fannonin shirin rage kangin talauci da bunkasa masana'antu.

A ranar 30 ga watan Maris ne, aka kawo karshen taron kasa da kasa kan raya wata sabuwar nahiyar Afirka karo na biyu a birnin Abidjan na kasar Cote D'Ivoire, inda jami'ai da kwararru daga kasashe da kungiyoyin duniya kusan 60 suka tattauna kan yadda za'a yi kokarin farfado da nahiyar.

A 'yan shekarun nan, kasar Sin na kara azama wajen zuba jari, da samar da rancen kudi, gami da bada tallafin fasahohi ga kasashen Afirka. A cewar Nicolas Rosellini, kasar Sin na zuba jari ga ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, ba ma kawai ta samar da dimbin guraban ayyukan yi ba, hatta ma tana kyautata tattalin arzikin kasashen Afirka daban-daban.

Nicolas Rosellini ya kara da cewa, hadin-gwiwar da hukumar UNDP ke yi da kasar Sin, za ta taimaka wajen cimma burin kawar da kangin talauci zuwa shekara ta 2030.

Kana Nicolas Rosellini, ya yabawa muhimmin shirin da gwammatin kasar Sin ke aiwatarwa a halin yanzu, wato fitar da daukacin mazauna karkara daga talauci zuwa shekara ta 2020, inda ya ce, akwai kasashen Afirka da dama wadanda suke sha'awar kara fahimtar yaya gwamnatin kasar Sin take yi don cimma wannan babban buri na kawar da talauci a tsakanin alummarta.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China