in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Koriya ta arewa da Amurka su cigaba da kokarin kawar da nukiliya daga zirin Koriya
2018-05-26 15:48:08 cri
Kasar Sin ta sanar a jiya Juma'a cewa tana fata kasashen Koriya ta arewa (DPRK), da Amurka za su cigaba da shirin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa, kana za su cigaba da kokarin kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang shi ne ya yi wannan tsokaci a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar na soke taron ganawar da aka shirya gudanarwa tsakanin shugaban na Amurka da takwaransa na Koriya ta Arewa.

Mista Lu ya ce, yunkurin da aka fara yi a 'yan kwanakin baya na shirya tattaunawa da kuma daidaita yanayin da ake ciki game da batun zirin Koriya al'amarin mai cike da tarihi, kuma ya kasance a matsayin wata babbar dama ta warware takaddamar siyasa.

Ya ce bangarorin biyu, wato Koriya ta Arewa da Amurka, sun bayyana aniyarsu na daukar matakan kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya ta hanyar tattaunawar sulhu da tuntubar juna, kuma bangarorin biyu sun nuna kwarin gwiwa game da wannan batu.

Lu Kang ya ce, matsayar gwamnatin Sin kan batun zirin Koriya al'amari ne dake bayyane a fili kuma bisa gaskiya, ya kara da cewa, kasar Sin ta yi amanna cewa tattaunawar shugabannin na Koriya ta Arewa da Amurka zai taka muhimmiyar rawa wajen kawar da shirin makaman nukliya daga zirin Koriyar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China