in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce akwai yiwuwar ganawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa ta gudana kamar yadda aka shirya
2018-05-26 15:40:27 cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana a jiya Juma'a cewa, akwai yuwuwar Amurka, ta dawo da ganawar da ta shirya yi a baya da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.

Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, suna tattaunawa mai ma'ana da Koriya ta Arewa, game da sake dawo da batun ganawarsu, kuma idan aka cimma nasara, ta yuwu taron ya gudana a ranar da aka shirya a baya, wato 12 ga watan Yuni mai kamawa.

Ya kara da cewa, idan kuma akwai bukata, to za a daga ranar.

Da farko a jiyan, Donald Trump, ya ce watakila taron ya gudana ranar 12 ga watan Yuni, yana mai cewa Koriya ta Arewa da Amurka dukkansu, na son ya gudana.

A ranar Alhamis ne shugaba Trump ya aike da wasika ga shugaba Kim, ya na mai sanar da soke ganawar da suka shirya yi.

Ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa, Kim Kye Gwan, ya ce a shirye kasarsa ta ke ta tattauna da Amurka a kowane lokaci, domin su warware matsalolin dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China