in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi maraba da kudurin da kwamitin sulhu ya zartas game da Koriya ta arewa
2017-12-23 13:13:30 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da da kuduri mai lamba 2397 da daukacin kwamitin sulhu na Majalisar ya zartas game da kara kakabawa kasar Koriya ta arewa takunkumi.

Wata sanarwa da Sakatare Janar din ya bayar ta bakin kakakkinsa, ta ce matakin na da muhimmanci kwarai, ga cimma burin tabbatar da rashin kasancewar nukiliya a zirin Koriya, da samar da kyakyawan yanayin warware matsalar ta hanyar diplomasiyya.

Koriya ta arewa ta kara yin gwajin makamai masu linzami a karshen watan Nuwamban da ya gabata ba tare da yin la'akari da kiraye-kirayen kasashen duniya da suka da matakin nata ba.

A jiya Juma'a ne kuma, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin mai lamba 2397, inda ya kayyade yawan tattacen mai da Koriya ta arewa ke shigowa daga ketare daga ganga miliyan 2 a kowace shekara zuwa dubu 500, kuma yawan danyen mai da kasar za ta shigar ma ba zai wuce ganga miliyan 4 ba a ko wace shekara, ban da wannan kuma, za a dawo da 'yan kasar dake kwadago a kasashen ketare a cikin wani lokacin da aka kayyade.

Baya ga haka, kudurin ya hana kasar fitar da kayakin abinci da injuna da kayayyakin lantarki da katako da kuma shigar da na'urorin masana'antu da na injina da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China