Game da kudurin ne kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta ce kasarta na fatan ganin bangarori daban-daban sun yi biyayya yadda ya kamata, ga kudurorin kwamitin sulhun game da Koriya ta arewa, ciki har da kuduri mai lamba 2397, don warware matsalar zirin.
Madam Hua ta kara da cewa, kudurin mai lamba 2397, ya kara daukar matakan saka takunkuman da suka dace ga Koriya ta arewa, a waje guda kuma ya jaddada cewa, bai kamata ba matakan su haifar da mummunan tasiri ga fararen hula da harkokin tattalin arziki da hadin kai da taimakon jin kai ba. Kana kudurin ya sake nanata kiyaye zaman lafiyar zirin Koriya da yankin arewa maso gabashin Asiya, ya na mai kira da a warware matsalolin ta hanyar diplomasiyya cikin lumana.
Baya ga haka, madam Hua ta ce, har kullum, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan tabbatar da rashin kasancewar nukiliya a zirin, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare da dagewa wajen warware matsalar ta hanyar tattaunawa.
A cewarta, Wannan shi ne matsayin da a ko da yaushe, kasar ke dauka game da batun. (Bilkisu)