A cikin sakon sa, shugaba Xi ya ce alakar kasar sa da Oman ta kai ga matsayin koli, inda ta shafi manya, kuma muhimman fannoni, karkashin inuwar shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, matakin da ya haifarwa al'ummun su alfanu mai tarin yawa.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, yana martaba alakar sassan biyu, yana kuma da burin daga matsayin ta, ta yadda za ta kai ga dama mai daraja da za ta amfani kasashen bisa hadin gwiwar sarkin na Oman. Ya ce wannan gaba ta cikar dangantakar kasashen biyu shekaru 40, wata dama ce ta cimma wannan nasara.
A nasa bangare kuwa, Sarki Qaboos cewa yayi, Oman a shirye take ta karfafa muhimmiyar alakar dake tsakanin ta da Sin, ta yadda hakan zai haifar da alfanu, da kuma biyan bukatun al'ummun kasashen biyu.(Saminu Alhassan)