in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jaddada muhimmancin tantance ayyuka a matakan jam'iyya da na gwamnati
2018-05-24 10:03:50 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar tantance ayyuka yadda ya kamata, a dukkanin matakai da suka jibanci jam'iyya da na gwamnati.

Xi Jinping wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya bayyana hakan ne, lokacin da ya jagoranci zaman farko na kwamitin tantance ayyuka a jiya Laraba.

Shugaban ya ce, akwai bukatar samar da managarcin tsarin bai daya, wanda yake da cikakkun manufofi masu karfi, da inganci, na sanya ido da tantance sahihancin ayyuka, matakin da zai kasance mai fa'ida ga cimma nasarar ayyukan jam'iyya da na gwamnati baki daya.

Xi, wanda kuma shi ne jagoran hukumar koli ta rundunar dakarun kasar Sin, shi ne kuma ke shugabantar kwamitin tantance ayyuka, ya kara da cewa, yin kwaskwarima a fannin tantance ayyuka, da samar da managarcin tsarin bai daya na gudanar da hakan, na da matukar alfanu wajen karfafa jagoranci a fannin tantance ayyuka.

Daga nan sai ya sake jaddada tasirin aikin tantance al'amura yadda ya kamata, yana mai umartar sassan da batun ya shafa, da su kara azama wajen samar da dukkanin abubuwan da ake bukata don cimma nasarar wannan muhimmin aiki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China