Shugaban kasar Sin Xi Jinping yana fatan zurfafa hadin gwiwa ta fannin shari'a bisa tsarin kungiyar hadin kan birnin Shanghai (SCO), domin yakar munanan laifuka da kuma warware rikice rikice yadda ya kamata.
Xi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban taron shugabannin kotunan koli na mambobin kasashen SCO karo na 13 wanda aka gudanar a yau Juma'a a birnin Beijing.
Xi ya ce, yana fatan dukkannin bangarorin za su hada kai wajen yakar munanan laifuka da warware rikice rikice yadda ya kamata, da nufin samar da kyakkyawan yanayi mai cike da bin doka don samun nasarar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da kuma raya shiyyoyin da abin ya shafa yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)