in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana adawa da shirin Amurka na sayarwa yankin Taiwan makamai
2017-06-30 19:41:17 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang ya shaidawa taron manema labarai a yau Jumma'a cewa, kasarsa na matukar adawa da shirin Amurka na sayarwa yankin Taiwan makamai, tana mai kira ga Amurkar da ta dakatar da duk wata yarjejeniyar cinikayyar makamai da yankin.

Lu kang ya ce, yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, kuma shirin da Amurka ke yi na sayarwa yankin makamai, ya sabawa yarjejeniyar kasa da kasa da kuma muhimman ka'idojin huldar kasa da kasa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China