Lu ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis, game da tambayar da aka yi a cewa, Amurka ta soke gayyatar da ta yiwa Sin na shiga atisayen sojan a yankin Pasific na shekarar 2018 bisa dalilinta na wai Sin ta gudanar da ayyukan soja a tekun kudancin kasar, Lu ya kara da cewa, ko Amurka ta gayyaci kasar Sin shiga atisayen soja ko a'a, ba za ta canza niyyar Sin na tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin takun ba. (Bilkisu)