Ta ce bisa tarihin duniya, an shaida cewa, rufe kofa zai rufe hanyar hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, don haka ya kamata a bude kofa da inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya.
A kwanakin baya, yayin da ake shawarwari game da tattalin arziki a tsakanin Sin da Japan, da tsakanin Sin da Indiya, Japan da Indiya sun nuna goyon baya ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa ka'idojin da aka tsara, suna masu cewa ya kamata a tabbatar da tsarin yin cinikayyar duniya cikin 'yanci karkashin jagorancin kungiyar WTO.
Shugabannin kasa da kasa da na kungiyoyin duniya daban daban, su ma sun nuna goyon bayan su ga wannan ra'ayi. A gun taron manema labarun da aka gudanar a ranar 17 ga wata, Hua Chunying ta bayyana hakan, yayin da ta amsa tambaya game da ko Sin ta samu goyon baya daga kasashen duniya da dama, yayin da mai yiwuwa matsalar cinikayya a tsakanin ta da Amurka ta kara tsananta?.
Hua Chunying ta yi nuni da cewa, Sin da Amurka manyan kasashen duniya ne, kuma sun yi hadin gwiwa sosai a fannin tattalin arziki, don haka ya kamata su girmama juna, da yin zama daidai wa daida da juna, da ci gaba da aiwatar da hadin gwiwa don samun moriyar juna. (Zainab)