A cewar Kim Kye-gwan, kafin ganawar shugabannin kasashen biyu, bai dace kasar Amurka ta fadi wasu kalaman ta da hankali ga daya bangaren da zai halarci ganawar ba. Matsayin da mai ba da taimako ga shugaban Amurka kan harkokin tsaron kasar John Bolton ya gabatar kwanan baya, inda ya ba da misali da "matakin kawar da nukiliya na Libya" bisa manufa "Yin watsi da nukiliya kana a ba da tallafi ", ba wata hanya ce dake bayyana burin daidaita lamarin bisa shawarwari ba. Ya ce, muddin ana son a kawar da makaman nukiliya a zirin koriya, wajibi ne a Amurka ta daina yiwa manufofin Koriya ta Arewa karan tsaye, da ma daina yi mata barazana. (Amina Xu)