in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi maraba da shirin DPRK na rufe tashar gwajin makamin nukiliyarta
2018-05-15 10:37:17 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yaba da shirin da kasar Koriya ta Arewa ke yi na rufe wurin da take amfani da shi wajen gwaje-gwajen makamanta na kare dangi.

Guterres wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba manema labarai a Vienna, ya ce ya yi maraba da wannan mataki, yana mai cewa, rufe tashar zai zama wani muhimmin tabbaci da zai karfafa gwiwar matakan da ake dauka game da samun zaman lafiya mai dorewa da ma ganin an kawar da makaman nukiliya a zirin na Koriya.

Babban sakataren MDDr ya kuma bayyana fatan cewa, za a kai ga cimma matsaya game da batun nukiliyar zirin Koriya yayin ganawar da aka shirya yi tsakanin shugabannin Amurka da na Koriya ta Arewan.

Shi ma shugaba Trump wanda ke shirin ganawa da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a kasar Singapore a watan Yunin wannan shekara, ya yaba da wannan mataki na Koriya ta Arewa.

A karshen mako ne dai kasar Koriya ta Arewar ta sanar da shawarar lalata tashar gwajin makamin nukiliyarta ta Punggye-ri dake karkashin kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China