in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zuba jari da ba da rancen kudi ga Afirka da fatan raya ayyukan more rayuwa da farko
2018-05-23 13:30:16 criA kwanakin baya, masaniyar nazarin tattalin arzikin Sin da Afirka dake ziyara da yin nazari a jami'ar John Hopkins ta kasar Amurka Liu Qinghai, ta yi nuni bisa kididdigar kiran nazarin Sin da Afirka da kwalejin nazarin harkokin kasa da kasa ta jami'ar ta yi cewa, Sin ta fi son raya ayyukan more rayuwa a Afirka, ba wai neman mallakar albarkatun ma'adinai ba. Zargin da wasu kasashe suka yi game da kasar Sin cewa tana kwace albarkatu a Afirka, da kara baiwa Afirka basussuka da sauransu ba shi da tushe.

A kwanakin baya, shugabar cibiyar nazarin tattalin arzikin Afirka ta kwalejin nazarin Afirka ta jami'ar horar da malamai ta lardin Zhejiang na kasar Sin Liu Qinghai wadda take ziyara, da nazari a jami'ar John Hopkins ta kasar Amurka ta yi nuni da cewa, a wadannan shekaru, tare da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da bude kofa ga kasashen waje, a kan samu zargin kasar Sin a duniya, kamar ra'ayin kwace albarkatu a Afirka, ra'ayin kara baiwa Afirka basussuka da sauransu. Amma bisa kididdigar da kungiyoyin masana na kasar Amurka ciki har da kwalejin nazari kan kasa da kasa ta jami'ar John Hopkins suka yi, an shaida cewa, Sin ta zuba jari da ba da rancen kudi ga Afirka, ta yadda ta fi son raya ayyukan more rayuwa da farko, ba kwace albarkatun ma'adinai ba. don haka, zargin da aka yiwa kasar Sin ba shi da tushe.

Game da zargin da kasashen yammacin duniya suka yiwa kasar Sin a fannin yin mu'amala tare da Afirka, Liu Qinghai ta bayyana fannoni hudu wadanda suka mayar da martani ga zargin. Ta ce,

"Na farko, sha'anin da Sin ta zuba jari kai tsaye a Afirka shi ne sha'anin gine-gine, ba sha'anin hakar ma'adinai ba ne. Na biyu, sha'ani mafi girma da Sin ta ba da rancen kudi a Afirka shi ne sha'anin gina ayyukan more rayuwa, ba sha'anin hakar ma'adinai ba ne. Na uku, kasashen Afirka da suka fi karbar rancen kudi daga kasar Sin ba kasashen da suka fi samar da albarkatun halittu ba ne. Na hudu kuwa, horar da kwararru ta taka muhimmiyar rawa yayin da Sin ke mu'amala tare da kasashen Afirka. Daga wadannan fannoni hudu, muna iya ganin cewa, Sin ta dora muhimmanci kan gina ayyukan more rayuwa, da horar da kwararru a Afirka, wadanda suka sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki a Afirka."

Game da rancen kudi da Sin ta baiwa kasashen Afirka, Liu Qinghai ta yi nuni da cewa, ko da yake yawan rancen kudin da Sin ta baiwa kasashen Afirka a wadannan shekaru ya karu, amma yawansu bai yi yawa ba bisa dukkan basussukan da kasashen Afirka suke bi. Liu Qinghai ta ce, ya yi bambanta da zargin da kasashen yammacin duniya suka yiwa kasar Sin a wannan fanni, rancen kudin da Sin ta baiwa kasashen Afirka ya taimakawa kasashen Afirka wajen rage basussukan da suke bi, kana zai sa kaimi ga bunkasa yawan GDP na kasashen Afirka, don haka an sassauta matsin lamba da kasashen Afirka suke fuskanta a wannan fanni. Liu Qinghai ta bayyana cewa,

"Sin ta fi ba da tallafin nata ta hanyar rancen kudi ga kasashen Afirka, wanda ruwansa ya yi kasa da na kasashen yammacin duniya, da sauran kungiyoyin duniya wadanda suke baiwa kasashen Afirka irin wannan tallafi. Kana kamfanonin gine-gine na Sin suna da fasahohin zamani da suke iya rage lokacin yin gine-gine, ta haka za a iya rage kudin da ake kashewa wajen gina ayyukan more rayuwa a kasashen Afirka, wanda hakan ya taimakawa kasashen wajen rage basussukan da suke bi."

Haka zalika kuma, Sin ta ba da rancen kudi ta hanyoyi daban daban don sa kaimi ga bunkasa yawan GDP na kasashen Afirka. Liu Qinghai ta bayyana cewa,  

"Rancen kudin da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka ya kyautata gina ayyukan more rayuwa a Afirka, wanda ya taimakawa bunkasa masana'antu da cinikayya. Kana ana iya shigar da sabbin kayayyaki ko sabbin fasahohi, wanda zai iya samar da ayyukan yi a kasashen Afirka." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China