in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron kolin Johnnesburge na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Afirka
2018-05-14 12:32:32 cri

Babban sakataren kwamitin gudanar da ayyukan da aka tsara na bangaren kasar Sin na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma shugaban sashen kula da harkokin Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin mista Dai Bing ya ce, akwai tsare-tsaren hadin kai da yawa da kasashen duniya ke tsarawa kan kasashen Afirka, amma a gaskiya ba a cika alkawari. Abu mai muhimmanci shi ne, a yi kokarin tabbatar da nasarorin hadin kai da aka cimma, tare kuma da cika alkawarin da aka dauka a zahiri.

Mista Dai ya bayyana haka ne a kwanan baya a yayin da yake zantawa da wakilan kamfanin dillancin labaru na Xinhua. Ga karin bayanin da wakiliyarmu Bilkisu ta hada mana.

A yayin zantawar mista Dai Bing, ya ce, wani abu na musamman da Sin ke gudanarwa a hadin kanta da kasashen Afirka, shi ne mai da hankali kan aminci da cika alkawarin da ta dauka. Dai ya kara da cewa, kasar Sin ta dauki jerin muhimman matakai na hada kai da kasashen Afirka a duk tarukkan dandalin tattaunawar hadin kai tsakaninta da Afirka, kuma ta cika alkawarin tabbatar da dukkan matakan. Wadannan nasarorin da aka cimma sun inganta ci gaban tattalin arziki da rayuwar al'ummar kasashen Afirka sosai, wannan ya sa Sin ta samu yabo da tabbaci daga wajen jama'ar kasashen Afirka da ma kasashen duniya, wannan ne ma muhimmin dalilin da ya sa aka cimma nasara kan dandalin tattaunawar hadin kan sassan biyu.

A watan Disamba na shekarar 2015, an shirya taron kolin na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a birnin Johnnesburge na kasar Afirka ta kudu, inda gaba daya bangarorin biyu suka amince da daga matsayin dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka zuwa matsayin na dangantakar abokantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kana za a gudanar da manyan shirye-shiryen hadin kai guda goma, wadanda suka shafi masana'antu da zamanintar da sha'anin noma. Domin tabbatar da nasarar wadannan shirye-shiryen yadda ya kamata, kasar Sin ta tsaida kudurin samar da tallafin kudi na dalar Amurka biliyan 60 don nuna goyon bayan shirin. Taron kolin na Johannesburge ya kuma tsara shirin ci gaban hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, da bude wani sabon babi na gudanar da hadin kan cimma moriyar juna da samun ci gaba tare a tsakanin bangarorin biyu.

Shekarar 2018, ita ce shekarar da ake kokarin tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron kolin na Johnnesburge. Mista Dai Bing ya ce, a bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi, an tabbatar da nasarorin da aka cimma a taron daga dukkan fannoni yadda ya kamata.

A fannin siyasa, kasar Sin da kasashen Afirka na kara yin cudanya a matakai daban daban. Shugabannin bangarorin biyu sun yi ta kaiwa juna ziyarar da ba a taba ganin irinta a tarihi ba, kana ana ci gaba da zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa. Wannan ya ba da muhimmiyar jagora a siyasance ga ci gaban dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da kuma inganta tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron kolin. Bayan taron kolin, kasar Sin ta kulla dangantakar abokantaka iri daban daban, ko daga matsayin dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka daya bayan daya. Baya ga haka, kasar Sin ta nada jakadan kula da harkokin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka na ma'aikatar harkokin wajenta, a nasu bangaren, kasashen Afirka sama da 40 sun nada masu kula da ayyukan tabbatar da nasarorin taron kolin na dandalin tattaunawar hadin kan sassan biyu

A fannin tattalin arziki kuwa, ana ci gaba da inganta hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya zuwa watan Maris na shekarar 2018, kasar Sin ta tabbatar da tallafin kudi da ya wuce kashi 90 cikin dari da ta yi alkawarin baiwa kasashen Afirka, da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 60, ciki har da ayyukan gina hanyar dogo a tsakanin Habasha da Djibuti, da hanyar dogo a tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Najeriya da dai sauransu. Wadannan manyan kayayyakin more rayuwa wasu sun riga sun soma aiki, wasu kuma ana kokarin kammala su. Baya ga haka, kamfanonin kasar Sin da dama sun tafi kasashen Afirka don zuba jari. Daga shekarar 2009 zuwa yanzu, kasar Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afirka shekaru 9 a jere, kana jimillar kudin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ta wuce dalar Amurka biliyan 100.

A waje guda kuma, hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin al'adu na karuwa. Yawan Sinawa da suka je yawon shakatawa a kasashen Afirka ya wuce miliyan 1 a ko wace shekara, kana kasar Sin ta ba da horo ga kwararru a fannin fasaha na sana'o'i daban daban na kasashen Afirka da yawansu ya kai dubu 162, da samar wa al'ummar Afirka sama da dubu 20 kudin tallafi.

Baya ga haka, ana ci gaba da karfafa hadin kai tsakanin bangarorin biyu a fannin zaman lafiya da harkokin kasa da kasa. Kasar Sin na kokarin tabbatar da alkawarin tallafin da ya yi wa kungiyar AU, wanda ya kunshi tallafin kudi na dalar Amurka miliyan 100 a fannin aikin soja. Haka kuma kasar Sin kasar da ta fi tura ma'aikatan kiyaye zaman lafiya zuwa Afirka a cikin zaunannun mambobin kwamitin sulhu na MDD. Bugu da kari, Sin da kasashen Afirka na hadin kai sosai a wasu muhimman batutuwan na kasa da kasa da na shiyya-shiyya, a kokarin kiyaye muradun bangarorin biyu da na kasashe masu tasowa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China