in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara daukaka hadin gwiwar Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi
2018-04-25 14:14:53 cri

A ranar 23 ga wata, jakadan kasar Sin a kasar Afirka ta kudu Lin Songtian ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a cikin 'yan shekarun baya, sakamakon tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma ziri daya da hanya daya, an kai ga daukaka hadin gwiwar da ke tsakanin sassan biyu zuwa wani sabon matsayi. Lubabatu na tare da karin haske.

A yayin da Mr. Lin Songtian, jakadan kasar Sin a kasar Afirka ta kudu ke zantawa da wakiliyar CRI, ya bayyana cewa, tun bayan shiga karni na 21, yawan cinikin da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ya karu daga dalar Amurka sama da biliyan 10 a shekarar 2000 zuwa biliyan 170 a shekarar 2017, sai kuma yawan jarin da kasar Sin ke zubawa a kasashen Afirka ya karu zuwa sama da dala biliyan 100 daga biliyan guda. Wato ke nan, a cikin shekaru 18 da suka wuce tun bayan da aka kaddamar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, yawan cinikin da ke tsakanin sassan biyu ya karu da ninki 17, a yayin da yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya karu da sau 100. Jakadan ya ce, "Sin da Afirka na da bukatuwa da juna, kuma suna samar wa juna dama. An sauya tare kuma da daukaka hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, wato daga yadda gwamnati ke jagoranci zuwa yadda kamfanoni da kasuwanni ke jagoranci. Daga yadda gwamnati ke samar da gudummawa zuwa yadda kamfanonin sassan biyu ke aiwatar da hadin gwiwar samun moriyar juna. Wato an daukaka hadin gwiwar zuwa wani sabon matsayi."

Nahiyar Afirka wani muhimmin zango ne kan hanyar siliki ta ruwa ta gargajiya. Tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya a shekarar 2013 kuma, an fara aiwatar da shawarar a kasashen Afirka ta kudu, da Habasha da Kenya, har ta kai ga an fara cimma nasara. Mr. Lin Songtian ya ce, "Kasar Afirka ta kudu ta shige gaba a wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya. A Habasha kuma, kasar Sin ta taimaka wajen samar da hanyar jirgi da ta hada birnin Addis Ababa da na Djibouti, hanyar kuma da ta taimaka ga ci gaban masana'antu. Sai kuma a kasar Kenya, a gani na, hanyar jirgi da ta hada birnin Mombasa da Nairobi ba ta isa ba, ya kamata a shimfida ta har zuwa Uganda da Rwanda, don a hada masana'antun kasashen nan uku, wanda hakan zai zama misali na hadin gwiwar kasashe masu tasowa."

Mr. Lin Songtian ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya ne, ta yin la'akari da moriyar bai daya ta 'yan Adam baki daya. Sai dai wasu kasashen yammaci sun ci gaba da rike ra'ayin mulkin mallaka, wadanda suka dauki wasu kasashen duniya, musamman ma na Afirka a matsayin moriyar da za a raba, abin da ya sa suke nuna shakku a kan shawarar ta ziri daya da hanya daya. Ya ce, "Mu Sinawa sabbin zuwa ne a Afirka. A shekarar 2000, yawan jarin da muka zuba a nahiyar bai kai dala biliyan guda ba, to, wane ne ke nan ya kwashe albarkatun Afirka? Masu mulkin mallaka na kasashen yammaci ne suka dade suna mallakarsu. Nijeriya kasa ce da ta fi albarkatun mai a Afirka, wadda kuma ita ce kasar da ta fi shigowa da tataccen mai a nahiyar, sai dai danyen mai da take fitarwa ba ya isarta wajen sayo tataccen mai daga ketare. To, wannan ne abun da muke kira kwace, kuma irin wannan mataki na mulkin mallaka har yanzu ba a daina ba."

A watan Satumbar wannan shekara, za a kira taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka a birnin Beijing. A furucin da ya yi game da taron, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya jaddada cewa, taron zai mai da hankali a kan hada kan kasashen Afirka wajen raya ziri daya da hanya daya, tare hada shawarar ziri daya da hanya daya da shirin samun dauwamammen ci gaba na MDD nan da shekarar 2030 da kuma ajandar AU nan da shekarar 2063, sa'an nan a hada shawarar da manufofin bunkasa na kasashen Afirka. A game da wannan, Mr.Lin Songtian ya bayyana cewa, "Taron koli na bana yana da muhimmanci, wanda zai kasance taron da za a tsara makomar hadin gwiwar sassan biyu a kan wani sabon matsayi da suka kai. Ya kamata Sin ta taimaka wa kasashen Afirka su tsara shirye-shiryensu na raya kasa, ta taimaka musu wajen bunkasa masana'antu da birane, da kuma samun dauwamammen ci gaba. Ina da kyakkyawan fata ga taron, kuma na gaskata cewa, nasarorin da muka samu cikin shekaru 40 da suka wuce wajen yin gyare-gyare a gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje, za su taimaka ga tabbatar da kyakkyawar makomar kasashen Sin da Afirka."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China