in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kan Sin da Afrika zai samar da sabuwar dangantakar moriya
2015-12-29 11:16:21 cri

Shekarar 2015 da ake shirin ban kwana da ita, za ta kafa wani babban tarihi, kasancewar a cikinta ne dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika ta samu nasarar kaiwa wani babban matsayi ta fuskar ci gaba.

Masana harkokin siyasa da masu sharhi kan al'amura sun tabbatar da cewar, a wannan shekara ta 2015, hadin kan dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afrika ya samu tagomashi.

Shekarar, ta fara ne da batun rattaba hannu kan yarjejeniyar huldar dangantaka wato MOU tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, a fannin inganta sufuri da cigaban masana'antu.

Yarjejeniyar wacce aka kulla da zummar farfadowa da kuma bunkasa ci gaban masana'antu da sufuri, ta hada da samar da hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya, da harkar jiragen sama a kasashen na Afrika. Wannan batu ne ma ya sa kasar Sin ta tura jakadanta zuwa kungiyar tarayyar Afrika wato AU, sannan ita ma AU za ta aika da nata jakadun a farkon shekara mai zuwa domin sa ido don tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar cikin nasara.

Kasar Sin ta sha gudanar da yunkuri iri dabam dabam da suka shafi tabbatar hadin kai da kulla dankon zumunci tsakanin ta da kungiyar AU, a hannu guda kuma, da su kansu daidaikun kasashen na Afrika.

Sabelo Gatsheni Ndlovu, Darakta ne a cibiyar Bincike ta Archie Mafeje kuma Farfesa a jami'ar kasar Afrika ta Kudu, ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta samu matukar bunkasuwa a shekarar 2015, kamar yadda aka yi tsokaci a lokacin taron karawa juna sani na birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, a yayin taron hadin kan Sin da Afrika wato FOCAC a farkon watan Disambar wannan shekara. Kuma shi ne karo na farko da aka taba gudanar da taron na FOCAC a nahiyar Afrika.

Farfesa Gatsheni-Ndlovu ya ce, wannan ya nuna a fili yadda kasar Sin ke ci gaba da bin sahihan matakai domin ci gaban dorewar kyakkyawar alaka tsakaninta da Afrika.

Taron dai ya tabo batun kaidojin da aka gindaya game da hadin gwiwar bangarorin biyu da suka hada da yin gaskiya, abokantaka, daidaito da kuma cin moriyar juna.

Wannan taro, yana da muhimmancin gaske a tarihin hadin kan dake tsakanin Sin da Afrika.

A lokacin taron ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya sanar da aniyar kasar na ware zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan 60, a matsayin tallafi don gudanar da muhimman ayyuka a Afrika cikin shekaru uku.

Ayyukan sun hada da inganta ci gaban masana'antu, da noma irin na zamani, da samar da kwarewa ga ma'aikata, da samar da kayayyakin more rayuwa da kuma inganta fannin kiwon lafiya a kasashen na Afrika.

Gatsheni-Ndlovu ya ce, kasar Sin ta bayyana aniyarta na daura danba wajen tabbatar da gagarumin ci gaba a nahiya Afrika, kamar yadda ta sanar da haka a yayin taron na FOCAC. Haka kuma kasar Sin ta lashi takobin taimakawa AU da Afrika, wajen ci gaban samar da kayayyakin more rayuwa. Wannan tamkar cika alkawarin da kasar ta jima da dauka ne, na agazawa Afrika a fannonin aikin gona da masana'antu.

Yazini April, wata kwararriya mai bincike, daga cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Afrika ta Kudu, ta ce, hadin kan dake tsakanin Sin da Afrika ya kai kololuwa a shekarar 2015.

Ta ce a shekarar 2015, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta kara dagawa sama, kuma wannan ya bayyana a fili karara yadda aminci da moriyar juna ke wanzuwa tsakanin bangarorin biyu. Gudanar da taron FOCAC tamkar wata alama ce dake tabbatar da wannan dangantaka. Ta ce, za'a iya tabbatar da hakan idan aka yi la'akari da yadda likafar taron ta daga, zuwa matsayin taron koli. Ta ce, hadin kan Sin da Afrika an kafa shi ne da zummar cin moriyar juna. Kasar Sin ta bayyana kanta a matsayin abokiyar hulda da ta jingina da takwarorinta. Ta ce idan kasar Sin ta yi alkawarin aiwatar da wani abu, ba ta yin kasa a gwiwa wajen cikawa. Kasar Sin ba kamar Bankin Duniya ko kasar Amurka ba ce wadanda za su yi ta cika da surutu da kuma jan kafa, wajen aiwatar da alkawarin da suka dauka, in ji Madam April.

A wajen taron na FOCAC, kasar Sin ta amince ta taimakawa AU wajen cimma Ajandar shekarar 2063 da ta gabatar, baya ga ci gaba da samar da kayayyakin more rayuwa.

A cewar April, salon gudanar da taron FOCAC ya sauya, kasancewar ba kasar Sin ce ta zartar da kuduri dangane da abubuwan da za'a aiwatar ba. Kasashen Afrika su ne ke da ruwa da tsaki wajen aiwatar da shirin, ta hanyar tuntubar juna a tsakanin shugabannin kasashen su.

A wannan shekara ne aka kafa wata cibiyar hadin gwiwa ta Sin da Afrika wato CAJAC a takaice.

Wannan cibiya aikinta shi ne karbar korafi da kuma warware duk wata takaddama da ta taso ba tare da zuwa kotu ba. Lauyoyi daga kasashen Sin da Afrika ne suka yi hasashen cewar, yayin da huldar cinikayya ke kara karfafa, akwai yiwuwar samun takaddama a tsakani, a don haka CAJAC za ta dauki alhakin warware duk wata takaddama da ka iya tasowa.

Da yake jawabi a yayin taron na FOCAC shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya ce hadin kan kasar Sin da Afrika ya kai wani babban mataki.

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Afrika ta kudu Maite Nkoana-Mashabane, ya ce taron na FOCAC ya bayyana karara makasudin kafa dandalin hadin kan Sin da Afrika, wadanda suka hada da rikon amana da amfanar juna ta hanyar hadin kai don cin moriyar tsakanin bangarorin biyu.

A shekarar da ta gabata, hada-hadar kasuwancin kasar Sin ya kai dala biliyan 220 da hannayen jari na dalar Amurka biliyan 32.4.

A shekarar 2015, ana sa ran hada-hadar kasuwancin kasar Sin za ta kai matakin dalar Amurka biliyan 300.

Kasar sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sabbin ayyukan tallafi kimanin 245. Sannan ta yafe basuka kimanin 156 da ake bin wasu kasashen Afrika 31. Bugu da kari, kasar Sin ta sanya hannu kan aikin tallafi a fannin kiwon lafiya a kasashen Afrika 41.

Shekarar 2015 ta kasance muhimmiya wajen ci gaban huldar dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China