in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka
2017-07-04 10:48:34 cri

Bayan da kasashen Afirka suka samu saurin bunkasuwar tattalin arziki a shekaru da dama, sai dai kuma a 'yan shekarun baya, sun gamu da 'yar matsala. Duk da haka wannan nahiya mai yawan matasa tana kyautata kwarewarta ta hanyar aiwatar da "ajandar aiki ta shekarar 2063" da zuba jari kan matasa, tare da kokarin zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin, da zummar ci gaba da kokarin raya tattalin arzikin nahiyar.

A jiya Litinin 3 ga watan nan ne aka bude taron koli karo na 29 na kungiyar tarayyar Afirka ta AU, taron da ke gudana a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda wasu jami'ai suka yi nuni da cewa, ana sa ran bunkasa sabuwar dinkuwar nahiyar Afirka mai wadata bisa tanade-tanaden da ke cikin "ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063", wadda aka tsara domin raya nahiyar cikin dogon lokaci, sa'an nan kuma ya zama wajibi a inganta hadin gwiwa da kasar Sin.

A shekarun baya, nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin yankunan da suka fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya, kuma tana da wata baiwa da Allah ya hore mata. Amma sakamakon rikicin kudi da koma bayan farashin kayayyaki masu yawa da makamantansu, ya sa saurin ci gaban tattalin arzikin Afirka ya dan ragu, kana kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasashen Nijeriya da Afirka da Kudu a shekarar bara sun taimaka wajen dakatar da bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar ta Afirka baki daya.

Rashin ci gaban tattalin arziki da kasashen Afirka suke fama da shi, bai dace da manufar da aka tanada cikin "ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063" ba, wato raya Afirka mai wadata. Kungiyar AU ta tsara wannan manufa ce a kokarin kara bunkasa masana'antun Afirka da dinkuwar nahiyar baki daya, da kuma inganta karfin Afirka ta fuskar yin takara a harkokin tattalin arziki da raya tattalin arzikin nahiyar ta hanyoyi daban daban.

Duk da haka wasu jami'an AU sun ce, matsalar da Afirka take fuskanta a yanzu ba ta raunana karfin zuciyar nahiyar wajen cimma manufarta ba. Yanzu kasashen Afirka sun samu ci gaba a fannonin kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba a nahiyar da shimfida tsarin hanyoyin dogo masu saurin tafiya da makamantansu.

Ban da haka kuma, batun matasa ya sake jawo hankali a yayin taron kolin. Kamar yadda shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat ya fada, matasa, su ne kashin bayan ci gaban nahiyar Afirka. Makomar nahiyar ta Afirka ta dogaro da yadda ake biyan bukatunsu da yadda za su cimma burinsu. Ya kara da cewa, kungiyar ta AU ta fahimci muhimmancin matasa a fannin bunkasuwar nahiyar ta Afirka, don haka a wannan karo taron na da taken "cin gajiyar bambance-bambance dake tsakanin kasashe ta hanyar zuba jari kan matasa".

Har ila yau, wasu jami'an kungiyar ta AU sun yaba wa gudummowar da kasar Sin take bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka, sun kuma yi nuni da cewa, ya zama wajibi kasashen Afirka su inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasar Sin yayin da suke kokarin cimma manufar da ke cikin "ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063".

Anthony Mothae Maruping, mamban kungiyar AU mai kula da harkokin tattalin arziki ya ce, mun gode wa yadda kasar Sin take zuba jari a Afirka. Kasashen Afirka da Sin suna hada kansu yadda ya kamata a fannonin zuba jari da raya ababen more rayuwar jama'a. Muna fatan za a zurfafa irin wannan hadin gwiwa.

Madam Josefa Sacko, mambar kungiyar AU mai kula da raya tattalin arzikin yankunan karkara da aikin gona ta bayyana cewa, muna himmantuwa wajen inganta hadin kai da kasar Sin ta fuskar aikin gona. Kasar Sin na da kyawawan fasahohi masu yawa a fannin raya aikin gona, kuma mun ci gajiya sosai.

Kamfanin ba da shawara na McKinsey ya kaddamar da rahoto a kwanan baya, inda ya ce, kasashen Sin da Afirka na samun saurin ci gaban huldar da ke tsakaninsu. Kamfanonin kasar Sin suna zuba Afirka jari a kasashen Afirka, taimaka mata da fasahar tafiyar da harkoki da karfin kirkire kirkire, lamarin da ya taimaka ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar ta Afirka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China