Shugabannin hukumomin tsaron kasa da na sojoji na kasashe membobin kungiyar SCO wato Rasha, Indiya, Kazakhstan, Kyrgyz, Pakistan, Tajikistan da kuma Uzbekistan, da kuma wakilan sashen sakatariyar kungiyar SCO, da kwamitin gudanarwa na yaki da ta'addanci a yankuna sun halarci taron.
A cikin jawabinsa, Wei Fenghe ya bayyana cewa, taken taron a wannan karo shi ne "kafa kungiya mai buri iri daya, da yin kirkire-kirkire, da hadin gwiwa don neman bunkasuwa tare". Ya ce kamata a aiwatar da ayyukan da shugabannin kasa da kasa suka cimma daidaito a kan su, da inganta hadin gwiwarsu a fannin kiyaye tsaron kasa.
Wei Fenghe ya yi nuni da cewa, ya kamata a ci gaba da bin tunanin Shanghai, da kara yin hadin gwiwa a fannonin mu'amalar dake tsakanin manyan shugabanni, da atisayen soja, aikin soja, horaswa da sauransu, musamman ma batun hadin kan wajen yaki da ta'addanci, don tabbatar da zaman lafiya a yankuna har ma a dukkan duniya gaba daya. (Zainab)